Sunday, 31 December 2017

Shahararrun wakokin shekarar 2017

A bangaren wakoki, mawaka da yawa sun yi kokarin fitar da sabbin wakoki  da suka nishadantar da mutane sosai, a wannan sunayen wakokin da muka fitar  da sukayi fice a wannan shekarar ta 2017, munyi la'akari da yawan ambatonsu da akayi a shafukan yanar gizo da kuma kallonsu da akayi a shafin youtube da kuma irin bazuwarsu tsakanin al'umma.Waka ta farko wadda ko baka tsaya ka jitaba zakaji wani na jinta, kuma babba da yaro ya santa, wakar ta bazu sosai tsakanin matasa da musamman mata, itace wakar Rariya wadda Umar M. Sharif da Khairat Abdullahi suka rera.

Wakar anyita dan fim din Rariya wanda tauraruwar fina-finan Hausa da aka kora, Rahama Sadau ta shirya, fitowar wakar tayi matukar tasiri sosai wajan tallar fim din.
Har ila yau wakar Umar M. Sharif ta jirgin so, wadda ya rera tare da Murja Baba, itace waka ta biyu da tafi watsuwa tsakanin matasa, wannan wakar an reratane a cikin fim din Mansoor, wanda kamfanin FKD ya shirya, Sabuwar jaruma, Maryam Yahaya da Umar M. Sharif, shima a matsayin sabon jarumi suka taka rawa sosai a wannan fim.


Sai kuma wakar Dauda Kahutu, Rarara, Sannu da sauka Baba Buhari, ya rera wannan waka kuma ya saketa a ranar da shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya dawo gida Najeriya daga doguwar jiyyar da yayi a kasar waje, an yita rade-radin cewa shugaban ya mutu, amma sai gashi ya dawo. Sakin wakar a lokacin ya kara mata amsuwa tsakanin mutane musamman masoyan shugaban kasar, anyita amfani da ita wajan nuna murnar dawowar shugaban kasar.
Wakar Nura M. Inuwa ta Ranar Aurena ta samu karbuwa sosai gurin matasa da, musamman yanmata, a wannan shekarar yayi aure haka kuma yayi wannan wakane dan godiya ga Allah da kuma godewa wadanda suka halarci auren nashi.
Sai kuma wakar Maza Bayanka, wadda mawaki Sadik Zazzabi ya rerawa tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso tare da Maryam Fantimoti,a wakar akwai shagube da ya yiwa gwamnan jihar Kano na yanzu, Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, duk da cewa be ambaci sunanshiba amma da yawa mutane sun fahimci dashi yake.

Sanadiyyar wannan waka an kama Sadik Zazzabi, wannan dalili yasa wakar tashi ta kara yin suna tsakanin mutane.


No comments:

Post a Comment