Monday, 11 December 2017

"Shanun shugaba Buhari sunga Canji: Sun kara kiba"

Jiyane shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya ziyarci gonarshi dake garin Daura kuma yayi fatan cewa 'yan Najeriya zasu rungumi harkar noma dan kasarmu ta rika noma abincin da zata rika ciyar da kanya, ba sai an shigo dashi daga kasashen waje ba.Bayan da hotunan ziyarar gonar tashi suka watsu, wasu sun zakulo hotunan ziyarar daya kai gonar tashi a shekarar 2015 da yaci zabe, sun kuma kwatantasu shanun da hotunansu na ziyararahi ta jiya inda sukace shanun sun kara kiba. Wai lallai sunga canji.


No comments:

Post a Comment