Tuesday, 19 December 2017

Shin uwargidan shugaban kasa, A'isha Buhari ta kawo sabon salon daukar hotone a cikin keke napep?

A satin daya gabatane akaga uwargidan shugaban kasa, Hjiya A'isha Buhari a cikin keke Napep/ a daidaita Sahu.. lokacin da taje garin Daura ta kuma rabasu ga matasa dan suyu sana'a, hoton na uwargidan shugaban kasar ya dauki hankulan mutane da yawa inda har wasu suka rika dangantashi da siyasa, to kwatsam sai gashi da alama 'yan mata, gwanayen daukar hoto zasu dauki wannan abin a matsayin wani sabon yayin daukar hoto.An sabadai ganin yawancin 'yan matan idan zasu dauki hoto na birgewa su tsaya kusa da wata mota me kyau ko kuma wani guri me daukar hankali, amma sai gashi a wannan hoton anga wannan budurwar cikin keke napep.
Hotunan nata sun birge, saidai dayake ba'a saba ganin irin hakaba, wasu zasu iya kiranshi da sabon salo.No comments:

Post a Comment