Saturday, 30 December 2017

Shugaba Buhari ya baiwa matattun mutane uku sabbin mukamai

A jiyane shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya nada wasu sabbin daractocin manyan ma'aikatan gwamnati su dari biyu da tara, saidai wani sabon labari daya fito kuma ya dauki hankulan mutane shine yanda aka samu  sunayen mutane uku da suka mutu a cikin sunayen da shugaban kasar yaba sabon mukamin.Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa matattun mutanen da shugaba Buhari ya baiwa sabbin mukaman na jiya sune:

Okpozo wanda ya mutu a watan Disambar shekarar data gabata, a Birnin Benin.

Sai kuma tsohon shugaban 'yan sanda Donald Ugbaja, wanda ya mutu a watan Nuwamba, shugaba Buhari ya nadashi a matsayin daya daga cikin shuwagabannin gudanarwa na hukumar kula da masu siyan kayan masarufi na kasa.

Sai kuma Christopher Utov, wanda shima ya mutu, shugaba Buhari ya bashi mukamin daya daga cikin masu gudanarwa na hukumar bincike akan harkar tattalin arziki da zaman takewa.


No comments:

Post a Comment