Friday, 29 December 2017

Shugaba Buhari ya dorawa jami'an tsaro lafin hadarin babur daya faru da danshi

Rahotanni sun bayyana cewa bayanda shugaban kasa, Muhammadu Buhari yaje ganin danshi, Yusuf da yayi hadarin babur, ranshi ya baci sosai ya kalleshi ya girgiza kai, ya dora laifin abinda ya faru akan jami'an tsaro, inda ya tambayi dalilin daya sa aka bar Yusuf din ya fita da dare haka.


Jaridar Thisday ta bayyana cewa, wasu manyan jami'an gwamnati da suka hada da ministan cikin gida sun tsaya tsayin daka wajan ganin likitoci sun baiwa dan shugaban kasar irin kulawar data kamata.

A wani sako da me daukar hoton shugaban kasar, Bayo Omoboriowo ya fitar, yace Yusuf  Buhari mutumin kirkine, kuma wannan tsautsayin ya faru dashi kwana daya bayan ya aikamai da sakon taya murnar kirsimeti, ya kara da cewa beji dadin hakanba, kuma yanamai fatan samun sauki nan bada dadewaba.

Muna fatan Allah ya sauwake.

No comments:

Post a Comment