Thursday, 28 December 2017

Shugaba Buhari ya gana da Abdulmumini Jibril

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya gana da dan majalisar wakilai daga jihar Kano, Abdulmumini Jibril dake wakiltar mazabar Kiru da Bebeji, wanda majalisar ta dakatar dashi na tsawon lokaci.Me baiwa shugaban kasar shawara ta fannin sabbin kafafen watsa labarai, Bashir Ahmad ne ya bayyana cewa shugaba Buhari yana ganawa da dan majalisar amma be bayyana me suka tattauna akaiba.

Abdulmumin Jibril ya dade yana bayyana cewa dakatarwar da aka mishi bata bisa ka'ida wanda yanzu haka batun yana kotu.


No comments:

Post a Comment