Friday, 1 December 2017

Shugaba Buhari ya sauka lafiya a kasar Jorda, kamin ya sauka daga jirgi, saida ya godewa matukin jirgin nashi

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sauka a kasar Jordan, inda yaje domin halartar taron gano hanyar magance ayyukan ta'addanci, wani abu dayabirge mutane da wannan tafiya ta shugaban kasa Muhammadu Buhari, shine, bayan jirginshi ya sauka a kasar Jordan, kamin ya sauka daga cikin jirgin, saida ya juya, ya gayawa matukin jirgin nashi cewa, Nagode.

Gwamnonin Osun, Kogi da Naija da kuma wasu manyan ma;aikatan gwamnatine suka yiwa shugaban kasa Muhammadu Buhari rakiya zuwa kasar ta Jordan.Muna fatan Allah yasa su gama abinda suke su kuma dawo gida Lafiya.

No comments:

Post a Comment