Sunday, 10 December 2017

Shugaba Buhari zai halarci taro akan dumamar yanayi a kasar Faransa

Shugaban kasa Muhammadu Buhari zaikai ziyarar aiki kasar Faransa idan Allah ya kaimu ranar Talata, 12 ga watan Disambarnan da muke ciki, shugaban zai halarci tarone akan yanda za'a samar da kudi dan magance matsalar dumamar yanayi.Kafin halartar taron anasa ran shugaban kasar zai halarci wata liyafar cin abinci da shugaban kasar Faransar, Emmanuel Macron zai shiryawa shuwagabanin Duniya da zasu halarci taron.

Kasar Faransarce da hadin gwiwar majalisar dinkin Duniya da kuma wasu kungiyoyi masu zaman kansu suka shirya wannan taro.

No comments:

Post a Comment