Sunday, 31 December 2017

Shugaban sojojin Najeriya, Buratai ya hau dutsen Aso Rock, Abinda wani shugaban soja bai taba yiba

Sojojin Najeriya sun dare saman fitaccen dutsen ‘Aso Rock’ sun yi atisaye
Rundunar Sojin kasar nan da ke kula da kan iyakar Birnin Tarayya Abuja sun kare ayyukan bana da hawa saman dutsen nan da aka sani watau na ‘Aso’. Sojojin sun yi hakan ne don motsa jikin su. A cikin Rundunar da tayi tattaki zuwa saman wannan dutse akwai Shugaban Hafsun Sojin Kasar Laftana Janar Tukur Buratai. Shugaban Bataliyan Sojin da ke gadin Garin Shugaban Kasa Manjo Janr MS Yusuf mai shirin barin gado ne ya gayyaci Janar Buratai.


Kamar yadda Mai magana da yawun Sojin kasar ya bayyana Birgediya Janar SK Usman, daga cikin wadanda su ka hau dutsen akwai wadanda ba Sojojin Kasa ba ba irin su Jami’an kula da hanyoyin kasa watau FRSC da kuma Sojin sama da na ruwa na Kasar. 

Dutsen dai yana da tsananin tsawo na akalla taku 34, 000 daga kasa kuma wannan ne karo na farko da Shugaban Hafsun Soji zai ja tawagar sa zuwa saman dutsen a tarihin Najeriya inji Birgediya Janar Sani Kukasheka Usman na Rudunar Sojin Kasar.
hausa.naija.ng

No comments:

Post a Comment