Tuesday, 12 December 2017

Shuwagabannin Izala sun dawo Najeriya daga kasashen turai inda sukaje yin da'awa

Shugaban IZALA Sheikh Abdullahi Bala Lau ya dawo Naijeriya. Da sanyin safiyar Talatan nan ne jirgin Da ya dauko Manyan Maluman IZALA daga Kasar Burtaniya ya sauka a babban filin sauka da tashin jirage Na Nnamdi Azikiwe dake birnin tarayya Abuja a Naijeriya.Jirgin wanda yake dauke da Shugaban IZALA Sheikh Abdullahi Bala Lau, tare da Sakataren
kungiyar Sheikh Kabiru Gombe, An hango babbansakataren Kungiyar Sheikh Kabir Haruna Gombe tare da shugaban Kungiyar Sheikh Abdullahi BalaLau sun sauko cikin fara'a suna ta fadin "Alhamdulillah" Wanda Alamu ke nuna sun samu
gagarumar Nasara a bulaguron da sukayi Na Aikin Da'awa a kasashen Turai. Muna maraba da dawowar ku, tare da Addu'ar  Allah ya karbi ibadun da akayi, ya Kara daukaka. Amin.

No comments:

Post a Comment