Tuesday, 19 December 2017

SOJOJIN NIJERIYA DAKE BARIKIN BOKAVU A KANO SUN KOKA KAN YADDA SAMARI BA SA ZUWA ZANCE WAJEN YA'YANSU

Babban limamin masallacin Juma'a na sojoji dake Barikin Bokavo a jihar Kano, ya ce suna da 'yan mata da yawa a Barikin su amma samari ba sa zuwa zance gurinsu.


Limamin ya yi wannan jawabin ne yayin da yake zantawa da 'yan jarida bayan kammala sauka na dalibansu guda 40 da ya gudana a Barikin, inda ya yi kira ga al'umma da su ringa zuwa neman aure a cikin Barikin.
rariya.

No comments:

Post a Comment