Sunday, 31 December 2017

Sunayen matattun mutanen da shugaba Buhari ya baiwa mukamai sun karu zuwa mutum takwas

Sunayen da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya baiwa mukaman shuwagabannin ma'aikatun gwamnatin tarayya daban-daban da ya jawo cece-kuce saboda samun kusan mutum uku da suka mutu a ciki, abin ya kara tsawo, domin kuwa wasu sabbin rahotanni dake fitowa sun bayyana cewa an samu karin sunayen mutum biyar, wanda hakan yakai yawan mutane takwas kenan da shugaban ya baiwa mukami da sun mutu.Sunayen matattun mutanen da shugaban kasa ya baiwa mukaman, kamar yanda jaridar Daily trust ta ruwaito sun hada da, marigayi Francis Okpoza, da marigayi tsohon mataimakin shugaban 'yan sanda, Donald Ugbaja da marigayi Rev. Fr. Christopher Utov, sai kuma marigayi Garba Attahiru da marigayi Umar Dange da marigayi Dr Nabbs Imegwu, sai marigayi Ahmad Bunza. na takwas dinsu jaridar tace bata samu tabbacin cewa ya mutumba amma ta samu kishin-kishin.

Jam'iyyar adawa ta PDP tace wannan fitar da sunayen matattu cikin sunayen da shugaban kasar yayi alamace ta rashin iya aiki, kuma tayaya mutanen da suka kasa tattara sunayen mutanen da za'a baiwa mukaman gwamnati yanda ya kamata zasu iya gudanar da lamurran cigaban al'umma na kasa?

Saidai a wata sanarwa da me magana da yawun gwamnatin, Garba Shehu ya fitar yace an tattara wadannan sunayenne tun shekarar 2015 data gabata lokacin tsohon sakataren gwamnati, Babachir Lawal, amma gwamnoni suka ki amincewa da sunayen dake ciki, wannan yana shugaban kasa ya nada wani kwamiti dan a sake duba sunayen, kuma an kammala wannan aiki tun shekarar 2016, amma saboda shugaba Buhari baya kasar, lokacin yana rashin lafiya shiyasa be samu damar dubawa da sanya hannu akan sunayenba.

Ya kara da cewa daga lokacin hada sunayen zuwa kammalawa APC ba zata hana mutane mutuwa ba, amma ya bayar da tabbacin cewa za'a maye sunayen matattun mutanen da masu rai.

Sannan kuma ya bayyana cewa babu wanda za'a hukunta dalilin wannan lamari daya faru.

Jaridar tace ta samu daga wata majiya, cewa abinda ya kawo wannan rudani shine, tsaikon da aka samu daga wasu gwamnoni na bayar da sunayen mutanensu da za'a baiwa mukaman, sannan kuma sunayen da aka fitar, da yawa daga ciki tun sunayen farkone da aka mikawa gwamnati kamin a sake dubasu.

Akwaidai rahotannin maimaita sunayen mutane fiye da daya a cikin sunayen da shugaban ya baiwa mukaman da kuma sunayen 'yan jam'iyyar adawa a ciki.
   

No comments:

Post a Comment