Saturday, 23 December 2017

Taurarin Fina-Finan Hausa sun zama jakadun jami'ar koyi da kanka ta NOUN

A yaune jami'ar koyi da kanka ta NOUN a takaice, reshen jihar Kano ta shirya wani taron bita akan muhimmancin jami'ar a tsakanin al'umma, jaruman fina-finan Hausa da dama sun halarci taron kuma wasu daga cikinsu sun samu zama jakadun wannan jami'a.Tsohuwar tauraruwar fina-finan Hausa, Mansurah Isah da Al'amin Chiroma da Samira Ahmad da Umar Gombe da Bello Muhammad Bello(General BMB) da Hamisu Lamido Iyantama na daga cikin wadanda suka samu zama jakadun wannan jami'a.
Muna tayasu murna da fatan Allah ya kara daukaka./ Amin.

No comments:

Post a Comment