Thursday, 14 December 2017

Tsohon dan kwallon kafa, Ronaldinho zai koma siyasa

Hoton Ronaldinho daga Reuters
Tsohon tauraron kwallon kafa, Ronaldinho Gaucho dan shekaru talatin da bakwai, daga kasar Brazil, wanda ya taimakawa kasarshi ta lashe kofin Duniya a shekarar 2002, kuma ya taimakwa kungiyar ta Barcelona, lokacin yana taka musu leda, taci kofin Laliga har sau biyu da kuma kofin zakarun turai sau daya, ya bayyana kudirinshi na shiga siyasa.

Ronaldinhon dai ya bayyana cewa zai tsaya takarar kujerar sanata na jiharshi ta Minas Geraise, kuma tuni har ya fara kama kafa da wani dan takarar shugabancin kasar ta Brazil domin cimma wannan buri nashi.

No comments:

Post a Comment