Sunday, 10 December 2017

Uche Secondus ya zama sabon shugaban PDP

An bayyana Uche Secondus a matsayin sabon shugaban babbar jam'iyyar adawa ta PDP, a babban taron da aka tsawon daren Asabar ana kidaya kuri'u. Da yake sanar da sakamakon zaben, shugaban kwamitin zabe, Mista Gabriel Suswam, ya ce Uche Secondus ya kayar da abokan takararsa uku bayan ya samu kuri'a 2000.


Haka zalika, an zabi Sanata Umar Ibrahim a matsayin sabon Sakataren jam'iyyar na kasa, kuma tuni aka rantsar da sabbin shugabannin don kama aiki.

Mahalarta babban taron dai sun zabi sabbin jami'an da za su ja ragamar jam'iyyar kan mukamai guda 21 ne.

Tun da farko dambarwa ta kunno kai bayan wasu sun yi zargin shirya magudi, lokacin da wata takarda ta rika zagaya hannun mahalarta taron dauke da jerin sunayen wasu 'yan takara.
bbchausa.

No comments:

Post a Comment