Saturday, 16 December 2017

Uwargidan mataimakin shugaban kasa, Dolapo tasha yabo saboda irin yanda ta gaishe da tsohon shugaban kasa, Yakubu Gowon a wannan hoton

Uwargidan mataimakin shugaban kasa, Dolapo Osinbajo tasha yabo a gurin mafi yawan mutane dalilin wannan hoton, ta durkusane tana gaishe da tsohon shugaban kasa, Yakubu Gowon lokacin da suka hadu a coci wajan bikin kirsimeti.Da dama sun bayyanata a matsayin mace me tarbiyya wadda tasan girman manya, wasu sunce ai ba wani abin mamaki bane dan tayi hakan, saboda dama ai haka ake tsammanin ta dayi.

Hoton dai ya karade shafukan sada zumunta da muhawara inda akayi ta bayyana mabanbanta ra'ayoyi akanshi.


No comments:

Post a Comment