Tuesday, 12 December 2017

Uwargidan shugaban kasa, Hajiya A'isha Buhari ta raba kayan sana'o'i da bude wani dakin kula da mata masu ciki a Garin Daura

A yau, Talatane, uwargidan shugaban kasa, Hajiya A'isha Buhari tare da rakiyar wasu matan gwamnonin jihohin kasarnan, ta sauka a garin Daura, inda ta raba kayan sana'o'i ga matasa dari biyar, kayan da ta rabawa mutanen sun hada da keken dinki, injin markade da keke napep/'yar kurkura/agwagwa da buje/a daidaita sahu.Haka kuma a yau din dai, uwargidan shugaban kasar ta bude wani dakin shan magani na mata masu ciki data gina me daukar gadaje hamsin a cikin babban asibitin garin Daura.
No comments:

Post a Comment