Monday, 25 December 2017

Wahalar man fetur: Mataimakin shugaban kasa, Osinbajo yakai ziyara gidajen mai

Mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo yakai ziyara wasu gidajan mai a garin Legas da yammacin jiya, Lahadi, dan ganewa idanshi irin yanda al'umma ke kafa da wahalar sayan man, ya tattauna da wasu dake kanlayin sayan man inda har ya shiga wani gidan man ya matsawa wasu mai din a cikin motocinsu.Ganinshi a gurin ya farantawa wasu masu niyyar sayan man rai.
A jiyane dai, bisa umarnin shugaba Buhari, Shugaban rukunin kamfanin mai na kasa, Maikanti baru da tawagarshi  suka fara zagayen gidajen mai dan ganin itin yanda ake wahalar sayar dashi.

No comments:

Post a Comment