Friday, 15 December 2017

Wani bursuna ya roki alkali ya barshi a gidan yari bayan da alkalin ya bayar da belinshi

Wani bawan Allah a jihar Anambra me suna Tobias yaki amincewa ya tafi gida bayan da alkali ya bayar da belinshi saboda dadewa da yayi a gidan yarin ba'a yankemai hukunci ba da kuma rashin lafiya dake damunshi.Bayan da alkali ya bayyana cewa ya bayar da belinshi, sai ya fadi kasa yana rokon alkalin cewa shi amai rai a barshi a gidan yarin domin yafimai zaman lafiya, saboda 'yan uwanshi su talatin sunyi alkawarin kasheshi idan ya koma gida, wai dama mahaifinshima su suka kasheshi suka kwace gonar gadonshi.

Alkali ya mikashi gurin 'yan sanda inda ya bukacesu da sukai Tobias gida, kuma a rika zuwa duk bayan watanni uku ana dubashi.

Hmmm kaji da yawa.

No comments:

Post a Comment