Friday, 8 December 2017

Wasu masoyan Rahama Sadau a kasar Cyprus sun shirya mata liyafa dan tayata murnar zagayowar ranar haihuwarta

A jiyane korarriyar, fitacciyar jarumar finafinan Hausa da turanci, Rahama Sadau tayi murnar zagayowar ranar haihuwarta, duk da bata Najeriya amma, acan kasar Cyprus, inda take saida jami'ar nan ta Eastern Mediterranean ta karramata ta hanyar shirya wani taro da aka tattauna akan zagayowar ranar haihuwar Ranamar.Haka anan gida Najeriya, 'yan uwanta, abokan aiki dana arziki sunta aika mata da sakonnin taya murna, daga cikin abokan aikinta na fina-finan Hausa, wasu da suka hada da Sadiq Sani Sadiq da sauransu sun shirya liyafa ta musamman dan taya jarumar murnar wannan tana, duk da bata nan.
A wadannan hotunan ma wasu masoyan Rahamarne dake can kasar ta Cyprus  suka shirya wata 'yar kwarya-kwaryar liyafa dan tayata murna.

No comments:

Post a Comment