Sunday, 31 December 2017

Wasu 'yan Arewa da sukayi abin yabo a wannan shekarar

Yayin da ya rage saura awannai mu shiga sabuwar shekarar 2018, munyi waiwaye dan duba wasu daga cikin 'yan Arewa da sukayi abin alfahari a wannan shekara da muke ciki ta 2017. Akwaisu da yawa amma wadannan ne muka samu damar kawowa.

A farkon wannan shekararne, cikin watan Fabrairu, tsohuwar ministar muhalli ta Najeriya, Amina J. Muhammad ta shiga ofishinta, ta kama aiki a matsayin sabuwar mataimakiyar sakataren majalisar dinkin Duniya, wannan abu ba karamin yiwa 'yan Najeriya, musamman mutanen Arewa dadi yayiba.

An ta mata addu'a da fatan Alheri.

Ga kwazo ga kyau: Yar Najeriya Amina Yuguda ta lashe kyautar BBC ta Komla Dumor (hotuna)
Haka kuma a wannan shekararce, Amina Yuguda, daga jihar Adamawa ta lashe kyautar BBC ta Komla Dumor, wacce ake baiwa dan jaridan da yayi fice a aikinshi, kafar watsa labarai ta BBC tana bayar da wannan kyautar karramawane domin tunawa da wani tsohon hazikin ma'aikacinta me suna Komla Dumor wanda ya mutu a shekarar 2014.

Mutane da dama sun taya Amina murna kuma suka mata addu'ar fatan Alheri.


A wannan shekararne aka samu hazikin soja, dan Arewa na farko daya lashe duk wata kyautar da ake karrama dalibi da ita a lokacin kammala makarantar horas da sojoji ta NDA, sojan me suna AB Bature ya sha yabo ta wajan kwazo da kyakyawar dabi'a da sanin makamar aiki a lokacin da yake karatu a makarantar.

Shima ya matukar birge mutane sosai akaita yaba mishi akan wannan kwazo daya nuna.

A wannan shekararce aka samu wani hazikin malamin jami'a dan Arewa daya samu aiki a wata jami'ar kasar Ingila me suna Sheffield Hallam, Dan shekaru 29, Dr Salihu Dasuki ya zama malami mafi karancin shekaru a wannan jami'a ta kasar Ingila. An yi ta taya Salihu murna, cikin wadanda suka tayashi murnar samun wannan matsayi hadda me magana da yawun shugaban kasa, Malam Garba Shehu.


No comments:

Post a Comment