Sunday, 3 December 2017

'Yan jam'iyyar PDP sun kaiwa Atiku ziyara

 A yau lahadi 'yan jam'iyyar PDP na yankin Arewa masogabashin Najeeiya suka kaiwa tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar ziyara, ya bayyana cewa zuwan nasu ya tunamai da irin abubuwan da sukayi tare a baya.

Atikun ya kuma yabi jam'iyyar PDPn inda yace yana farinciki ganin cewa jam'iyyar ta kama hanyar komawa akan salinta.

Atikun dai ya fice daga jam'iyya me mulki, APC inda ya bayyana ta da cewa ta kasa cikawa 'yan Najeriya alkawuran data daukar musu. Kuma dama tuni anata rade-radin cewa PDPn Atiku zai koma.

No comments:

Post a Comment