Thursday, 14 December 2017

'Yan wasan kwallon gabar ruwa na jihar Kebbi sunzo na biyu a wata gasar cin kofi ta kasa da kasa da aka buga a birnin Legas

Tawagar 'yan wasan kwallon gabar ruwa na jihar Kebbi kenan a cikin jirgi lokacin da suke dawowa daga jihar Legas inda suka buga wata gasar cin kofi da aka saka, duk da basu yi nasarar cin kofin ba amma sunzo na biyu, bayan da sukayi rashin nasara a hannun kungiyar 'yan kwallon gabar ruwa ta Arsenal daga kasar Ingila.Ranar Lahadin data gabatane aka buga gasar a birnin Legas, 'Yan wasan kwallon gabar ruwan na Jihar Kebbi sun buga wasanni da kungiyoyi biyu, Pepsi Academy da Gidi Sharks kuma duk sun doke su, a wasan karshene suka buga da kungiyar Arsenal da sukazo daga Ingila amma si sukayi rashin nasara. Duk da haka za'a iya cewa sun taka rawar gani, tunda har sun kai wasan karshe, muna tayasu murna.


No comments:

Post a Comment