Wednesday, 6 December 2017

Yanda masu garkuwa da mutane suka sace jarumin fim din Hausa Al-Amin Buhari

A jiyane labari ya bazu cewa masu garkuwa da mutane sun sace tauraron fina-finan Hausarnan, watau Al-Amin Buhari, kamar yanda kafar watsa labarai ta Rariya ta wallafa, tace tayi magana da daya daga cikin masu ruwa da tsaki a harkar fim din kuma ya tabbatar mata da faruwar lamarin.
An sace Al-Aminne ranar Lahadi,  Kusa da garin Keffi, akan hanyarshi ta zuwa Jos daga Abuja, kuma saida aka biya kudin fansa, naira dubu dari biyar sannan aka sakoshi.

Yanzu dai rahotanni sun bayyana cewa jarumin yana birnin tarayya Abuja, amma yau Laraba ake tsammanin zai tafi Jos, Allah ya kiyaya hanya, ya kuma tsare na gaba.


No comments:

Post a Comment