Saturday, 16 December 2017

Zahara Buhari ma tayi murnar cikarsu shekara daya da yin aure: "Nima Nayi dace da miji na kwarai">>injita

A jiyane mukaji labarin mijin diyar shugaban kasa, Ahmad Indimi yayi murnar cikarsu shekara daya da yin aure, inda ya kara jaddada soyayyarshi ga matar tashi Zahara Buhari kuma ya bayyana cewa yana alfahari da kasancewa mijinta, itama ta fitar da makamancin irin wancan sakon nashi.A cikin sakon nata, Zahara Buhari ta saka wannan hoton na sama da ake gani inda ta bayyana cewa, wannan hoton ya bayyana duk wani abu da nike shirin fada, (Mijina) ka nunamin tsantsar soyayya, ka girmamani kuma kayimin halin kirki/saukin kai, Manzon Allah Annabi Muhammadu (S.A.W) ya fada cewa " mafi alkhairinku shine wanda yake kyautatawa iyalanshi" nagode Allah nasan kana cikin su(mafiya alherin mutane). Ta kara da cewa itama ta zama cikakken mutum data sameahi a matsayin mijinta kuma itama tana sonshi kuma sun dace da juna.

Muna musu fatan Alheri.No comments:

Post a Comment