Tuesday, 5 December 2017

Zuwan Shugaba Buhari Kano: Ba jirgi ya kamata ya hauba: Ta titi ya kamata yabi

Wasu 'yan Najeriya, sun fara kira da cewa, ziyarar da shugaban kasa, Muhammadu Buhari zaikai Kano gobe, kamata yayi yabi ta titi bata jirgin sama ba, dalilinsu kuwa shine, dan yaga irin yanda titin ya lalace da kuma talakawa ke shan wahala, harma da rasa rayuka akan titin.


Haka kuma, wadanda ke yin irin wannan kira, sunce bin hanyar titi zuwa, Kano zai kara tunawa shugaba Buhari halin da talakawa suke ciki. Dan watakila rabonshi da yabi titin tun bayan da ya hau kujerar shugaban kasa.

No comments:

Post a Comment