Monday, 8 January 2018

A boye dan shugaban kasa, Yusuf Buhari ya sayi babura biyu masu dankaren tsada: Dalilin hadarin nashi an kori masu tsaron lafiyarshi daga aiki

Wasu sabbin rahotanni dake fitowa danganeda hadarin babur da dan gidan shugaban kasa, Yusuf Buhari yayi wanda yayi sanadiyyar karyewa a kafa da kuma jin rauni a kai na cewa dan shugaban kasar ya sayi baburan tseren biyune masu dan karen tsada a asirce sannan kuma ya boyesu a gidan abokinshi, yake fita da dare a sace ba'a sani ba suna tsere.Kafar watsa labarai ta Daily Post ta bayyana cewa ta samu labari daga majiya me karfi daga fadar shugaban kasa kan yanda lamarin ya kasance, tace baburan guda biyune Yusuf Buhari ya siya a asirce kirar BMW wanda kowane daya kudinshi sunkai dalar Amurka dubu dari da hamsin da bakwai, idan aka hada biyun zasu baka kwatankwacin sama da naira miliyan dari kenan.

Bayan ya sayi baburan sai ya kaisu gidan abokinshi, Bashir Gwandu dake Gwarinpa A babban birnin tarayya Abuja, ya boyesu acan, akwai masu tsaron lafiyarsa na ma'aikatan farin kaya su uku sai ya shirya dasu suka rika barinshi yana fita da dare suna zuwa yin tsere da abokinshi cikin dare, ba tare da an sani ba a gida.

Wannan dalilin yasa ran shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya baci sosai, da farko dai an dakatar da masu tsaron lafiyar dan shugaban kasar ne amma daga baya sai aka koresu daga aiki baki daya.

No comments:

Post a Comment