Monday, 8 January 2018

A jiyane aka shaida ranar tafiyar shiririta ta Duniya

A jiyane, 7 ga watan Janairu, shekarar 2018, aka shaida ranar yin tafiyar shegantaka ta Duniya karo na shida, anyi wannan tafiyanar shegantaka a kasashen Czech Republic da Iceland, masu shirya wannan shiririta, wata kungiyace ta wasan barkwanci a kasashen turai me suna Monty Python, sunce tafiyar shegantakar ta wannan shekarar ta samu cigaba sosai domin mutane dari biyu da hamsin suka shigaaka yita dasu a kasar ta Czech Republic.Wanda ya shiryata shine Adam Jondara, mataimakin ma'aikatar tafiyar shiriritar da kuma Dan Masek, sakataren ma'aikatar. A kasar Icelanda ma, wanda ya shirya wannan tafiya, Lisa Og Bjarki, tayi kokarin gamsar da mahukunta har suka yarda suka saka wasu alamu na yin tafiyar shiriritar a gefen titi, inda masu tafiya a kasa kebi, haka kuma mahukunta birnin ReykJavik inda akayi wannan tafiya, sun sadaukar da wannan rana ga mutane da kungiyoyi masu taimakawa masu fama da tabin hamkali.
Wanda ya jagoranci wannan tafiyar shiririta a kasar ta Iceland, shine Hrannar Jonsson, shugaban hukumar kula da masu tabin hankalai na kasar, inda yayi tafiyar shiriritar, sannan jama'ar gari suka bishi a baya.
Rahotanni sunce har shugaban kasar ta Iceland shima saida ya taba.

No comments:

Post a Comment