Saturday, 13 January 2018

A karin farko a tarihin kasar Saudiyya: An baiwa mata damar shiga filin kwallo dan kallon wasa kaitsaye

A karin farko cikin tarihin kasar Saudiyya an bar mata sun shiga kallon wasan kwallon kafa kaitsaye a filin kwallon sarki Abdallah dake Jidda jiya Juma'a,  a warewa matan kofar shiga tasu daban data maza da kuma gurin zama naau daban, saidai wadanda suka zo da mazansu ko muharramansu, 'yan uwa, zasu iya zama a guri daya.Wannan wani yunkurine na baiwa mata 'yancin shiga abubuwan harkar rayuwa da Yarima me jiran Gado, Muhammad Bin Salman ya dauka dan kawo canjin irin yanda ake gudanar da rayuwa a kasar, a cikin wannan shekararne watan Yuni mata zasu fara tukin mota a kasar.
Mata da yawane suka taru suka shiga kallon wasan da aka buga tsakanin kungiyoyin wasan kwallon kafa na kasar ta Saudiyya, Al-Ahli da Al-Batin da yammacin jiya Juma'a. Kasar ta Saudiyya ta kashe makudan kudi wajan gina kayatattun filayen wasa lokacin kudin man fetur yana da tsada sosai a lasuwannin Duniya kamar yanda Daily Mail ta kasar Ingila ta ruwaito.
A yau Asabarne ake sa ran babban filin wasan kasar ta Saudiyya dake Riyad shima zai baiwa mata irin wannan dama ta shiga sukalli wasa kaitsaye.

Saidai wasu 'yan kasar sun soki wannan mataki a shafukan sada zumunta da muhawara inda suka rika cewa mata kamata yayi su kasance a gidan mazajensu suna kula da yara da kuma kyautatawa mazajensu dan neman yardar Allah bawai a filin wasa inda maza ke iface-iface da maganganun da basu daceba.

No comments:

Post a Comment