Monday, 1 January 2018

"A wannan shekarar za'a daina shigo da shinkafa daga kasashen waje">>Shugaba Buhari

A jawabin da yayi na sabuwar shekara, shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya fara da gaishe da 'yan Najeriya ya kuma tayasu murnar shiga sabuwar shekarar 2018, ya kara da cewa maganar canjice zata zama abu mafi muhimmanci a wannan sabuwar.

Ya kumace yayi matukaicein ganin cewa da yawan 'yan Najeriya a lokacin  hutun sabuwar shekara da kuma bukuwan Kirsimeti, memakon su zama cikin farin ciki sai aka sakasu cikin kunci, yace lokacine na nuna soyayya da tausayi ga mutane amma sai wasu 'yan Najeriya suka zabi saka mutane cikin wahalar man Fatur ta ba gaira babu dalili.Ya ce ya lura da yawa basu samu damar yin tafiye-tafiye ba kamar yanda aka saba, wadanda kuma suka samu yin tafiya, sun biya kudin mota da tsada, ya kara da cewa wannan ba abubane da za'a amince da shiba domin hukumar kula da harkar man fetur, kamfanin NNPC, yana kokarin ganin man ya wadata a gidajen mai, kuma ana kokarin ganin an gano wadanda suka assasa wannan wahalar mai dan hukuntasu.

Yace wannan matsala ba zata kawar da hankalin gwamnatinshiba akan abinda ta saka gababa na kawo canji a Najeriya, yace dole mu canja yanda muke yin abubuwa idan ba hakaba za'a barmu a baya a kokarin ganin an cire ''yan Najeriya daga kangin talauci zuwa kan turbar cigaban rayuwa.

Ya ci gaba da cewa, jawabinshi na wannan safiya zai mayar da hankaline wajan yiwa 'yan Najeriya bayanin yanda gwamnatinshi take kokarin ganin magance matsalolin abubuwan cigaban rayuwa da ake fama dasu a kasarnan.

Yace zasu baiwa maganar gina hanyoyi da titunan jiragen kasa da kuma maganar wutar lantarki muhimmanci, yanzu haka ana kan ginin titin jirgin kasa daga Kano zuwa Legas.


Shugaban kasar yace za'a gina titunan jirgin kasa a sassa daban-daban, kudanci da Arewacin kasarnan wadanda wasu za'a gamasu zuwa shekarar 2019 wasu kuma zasu wuce haka. Cikinsu akwai daga Kano zuwa Nijar, akwai wanda akeyi na zamani a cikin garin Abuja, sannan akwai jirgin kasa daga Kaduna Zuwa Abuja wanda shugaban kasar yace za'a karamishi tarago wanda zai rika daukar mutane da yawa, dadai Sauransu.

A fannin wutar lantarki kuwa shugaban kasar yace mutane da yawa zasu shaida cewa an samu cigaba, domin an samu habakar wutar da ba'a taba samun irintaba, ya kara da cewa hadin kan da sukayi da kamfanonin raba wutar lantarkin masu zaman kansune ya kara kawo saukin samar da wutar lantarkin, sannan akwai ayyukan kara cigaba da samar da wutar dan ta kara samuwa ga 'yan Najeriya da akeyi, misali, aamar da wutar lantarki ta hasken rana ta akeyi a jihar Katsina wanda tuni ya fara aiki kuma za'a kammalashi a wannan shekarar da kuma samar da wutar lantarki a Kaduna wanda shima ana kan aikinshi da sauran gurare na kasarnan.

Maganar noma kuwa shugaban kasar yace, shekarar data gabata ya gayawa 'yan Najeriya su rungumi harkar noma, kuma sun runguma saboda haka yana godemusu, ya kara da cewa harkar noma ta taimaka wajan cigaban tattalin arzikin Najeriya, kuma yayi alkawarin cewa a wannan shekarar da muke ciki za'a daina shigo da shinakafa kasarnan, za'a rika amfani da wadda manoman kasarnan ke nomawa a gidajenmu.

Ta bangaren tattalin arziki kuwa shugaban kasar yace a wannan shekararne Najeriya ta fita daga matsin tattalin arziki da tashiga sanadiyyar rikon sakainar kashi da gwamnatocin da suka gabata sukawa harkar tattalin arzikin.

Maganar siyasa kuwa shugaban kasar yace, yakamata 'yan siyasa su daina amfani da addini ko bangaranci wajan tallata kawunansu, ya kumace maganar canja fasalin kasa 'yan Najeriya basu da hakuri, suna son samun cigaba cikin sauri fiye da yanda zai iya faruwa a zahiri, lura da irin abubuwan da kasar ke dashi da kuma abinda zata iyayi, yace za'aji ra'ayoyin 'yan Najeriya akan canja fasalin kasa, tunda duk wani tsari da mutumne ya zauna ya yishi dole akwai kuskure a ciki amma shi a nashi ra'ayin yana ganin yin aiki a zahiri zaifi kawo cigana fiye da canja fasalin kasar.

Ta bangaren tsaro kuwa, shugaban kasa, Muhammadu Buhari yace, an dade da gamawa da Boko Haram, yanzu abinda ke faruwa harine irin wanda mugu ke tsayawa ya tsara, wanda kuma irin wannan yana faruwa a duk kasashen Duniya, koda kasashen dake da tsarin tsaro masu karfi sosai suna fama da irin wadannan matsaloli, idan aka duba kasashen turawa, larabawa dama waau kasashen  Afrika za'a ga ana samun irin wadannan hare-hare na sari ka noke, amma yace jami'an tsaro zasu cigaba da ganin sunyi abinda ya kamata dan kawo dawwamammen zaman lafiya, ya kara da cewa maganar garkuwa da mutane da take shirin zama ruwan dare itama za'a maganceta.

Shugaban kasar ya godewa jami'an tsaro bisa kokarinsu wajan magance matsalolin tsaro da kuma kokarin ganin an kawo zaman lafiya dan kowa da kowa ya samu yin harkokinshi yanda ya kamata.

A karshe shugaba Buhari ya kara nanata godewa 'yan Najeriya bisa addu'o'in da auka mishi lokacin yana kwance bashi da lafiya yace yana godiya sosai.

A karshe ya kara taya 'yan Najeriya barka da sabuwar shekara.

No comments:

Post a Comment