Monday, 8 January 2018

Abin birgewa: Bayeraben Legas ya auri bahaushiyar Kano

Soyayya ruwan zuma, idan dai da so na gaskiya, to babu wani abinda zai hana mutum kasancewa da masoyinshi, launin kalar fata, yare, kabila, kudi ko talauci, indai akwai soyayya ta gaskiya takan shafesu, a wadannan hotunan, wani Bayerabene dan jihar Legas tashi tazo daya da Bahaushiya, 'yar Kano, har Allah yasa aka daura musu aure.Hotunan wadannan masoya sunyita yawo a shafukan sada zumunta da muhawara anata saka musu albarka a wannan aure da sukayi da ba kasafai aka cika ganin irinshi ba. Muma muna musu fatan Allah ya tabbatar da Alheri ya basu zuri'a dayyiba.
No comments:

Post a Comment