Sunday, 21 January 2018

Abin birgewa: An dauki musulma me rufe gashin kanta tallar man gyaran gashi: Itace ta Farko

Mata masu rufe kawunansu da dan kwali da Hijabi, Allah ya san daku, Duniya ma ta fara baku Muhimmaci, a kwanakin bayane mukaji labarin wata ba'amurkiya da akayi 'yar tsana me Hijabi ta farko a Duniya dan karramata saboda saka Hijabi da take duk da cewa tana wasannin motsa jiki.


Haka kuma munji yanda kamfanin NIKE a shekarar data gabata shima yayi Hijabi ga mata musulmai masu motsa jiki . Anan ma wani kamfanin sayar da kayan kwalliya na matane da suka hada da Kayan Gyaran gashin kai na kasar Faransa me suna L'Oreal yayi abinda ba'a saba ganiba. Inda ya dauki wata me watsa labarai ta kafar Youtube kuma musulma me son rufe gashin kanta me suna Amina Khan ta zama daya daga cikin jakadunshi dake tallata kayan gyaran gashin kamfanin.

Abin ya dauki hankulan mutane da dama, dan an saba ganin masu tallar kayan gyaran gashi da kai a bude suna kwarkwasa amma gata ita kanta a rufe, ta bayyanawa manema labarai cewa rufe kansu da suke a matsayin musulmai bawai yana nufin basu damu da gyaran gashinsu bane, suma suna da matsalar gashi kamar kowace mace kuma suna kula dashi.

Anta yabawa Amina da kuma kara karfafamata gwiwa da kuma godemata da irin wannan namijin kokari datayi na karfafawa masu saka hijabi gwiwa, Duniya tayi dasu.
CNN.

No comments:

Post a Comment