Tuesday, 30 January 2018

Ahmad Musa ya koma tsohuwar kungiyarshi ta CSKA Moscow

Tauraron dan kwallon Najeriya dake buga wasa a kungiyar Leicester dake kasar Ingila, Ahmad Musa ya koma tsohuwar kungiyarshi ta kasar Rasha, CSKA Moscow akan aro, musan dai zai zauna a wannan tsohuwar kungiya tashi har zuwa karshen kakar wasan 2018.Musa ya je Leicester a kan tsabar kudi Euro miliyan shashida amma kuma sai ya rika shan zaman benci domin kuwa baya samun buga wasa. Musa ya nuna jin dadinshi sosai akan komawarshi tsohuwar kungiyar tashi inda ya bayyana cewa ya godewa Allah ya koma gida.
Muna tayashi murna.

No comments:

Post a Comment