Wednesday, 10 January 2018

Ali Nuhu da Adam A. Zango ku jawa magoya bayanku masu zagin mutane akanku kunne kafin ta baci: Abin ya isheni">>Tijjani Asase

Tauraron fina-finan Hausa, Tijjani Asase ya yi kira ga abokan aikinshi Ali Nuhu da Adam A. Zango akan cewa yana basu shawarar da su yiwa masoyansu magana wadanda da zarar wani abu ya hadasu da wani kawai sai su taso suna zagin manyan mutane, Tijjanin yace  koda abokan 'yan wasanne suke abu tsakaninsu sai yaran su rika saka baki suna zagi, yace, abin ya isheshi haka.
Gadai sakon da Tijjani ya saka a dandalinshi na sada zumunta:

"Shawara ga Ali Nuhu da Adam A zango yakamata kurika yiwa magoya bayan Ku magana wajen tayaku fada idan wani ya tabaku koda Abokin kune sai yaro ya fito midiya yana zagin mutane basukadai bane suke kaunarku kamar ni Tijjani Asase ina tare da Ali kuma ina tare da adamu musali sai suyifada idan kazagi Ali bazan jidadiba hakama Adamu yakamata mu Gyara tun da wuri Kafintabaci dan Gaskiya abin ya isheni zaginda yara suke wa manya ra'ayinane wanna ba na wani ba".

No comments:

Post a Comment