Tuesday, 30 January 2018

An dage dokar hana wa baki musulmi shiga Amurka

Kasashe 11 da gwamnatin Trump ta haramta wa shiga Amurka, yanzu suna iya shiga kasar bayan dage haramcin. Sai dai kuma 'yan kasashen da gwamnatin Trump ta kira masu hadarin gaske, yanzu za su fuskanci bincike mai tsanani.


Sakatariyar tsaron kasa Kirstjen Nielsen ta ce duk wanda ya nemi shiga Amurka zai fuskanci sabbin matakan tsaro.

Ta ce abu ne mai muhimmaci su tantane duk wanda zai shiga kasar.

"Matakan tsaron da aka dauka za su yi wahala ga bata-gari, kuma matakai ne da za su tabbatar da tsaron kasa", a cewar Jami'ar.

A watan Oktoban bara ne gwamnatin Trump ta sanar da haramtawa 'yan gudun hijira daga kasashen musulmi 10 da kuma Koriya ta arewa shiga Amurka.

Tun daukar matakin, 'yan gudun hijira 23 ne kawai daga kasashen suka shiga kasar, lokacin da alkalin wata kotu ya dage haramcin.

Ko da yake ba a ambaci sunayen kasashen da matakin yanzu ya shafa ba, amma tuni ya yi tasiri ga 'yan gudun hijirar kasashen Masar da Iran da Iraqi da Libya da Mali da Koriya ta arewa da Sudan ta kudu da Sudan da Syria da Yemen.
bbchausa


No comments:

Post a Comment