Monday, 22 January 2018

An rantsar da George Weah a matsayin sabon shugaban kasar Liberia

A yaune aka rantsar da tauraron dan kwallon kafa, George Weah a matsayin sabon shugaban kasar Liberia shine dai shugaban kasa na 24 kuma zai gaji mace ta farko data taba zama shugabar kasa a Nahiyar Afrika, Ellen Johnson Sirleaf. Rantsarwar data gudana a babban birnin kasar, Monrovia, a yau Litinin, ta samu halartar mataimakin shugaban kasar Najeriya, Farfesa Yemi Osinbajo da kakin majalisar dattijai Bukola Saraki  na daya.A wani sako daya fitar, Bukola Saraki ya bayyana wannan rana a matsayin be cike da tarihi kuma ya yiwa sabon shugaban kasar Fatan Alheri.
Ga kadan daga abinda bbchausa suka bayyana akan sabon shugaban kasar:

Iyayen George Weah talakawa ne.
Amma kwarewarsa a fagen tamaula ne ta kwace shi da iyalansa daga talauci.
Dan wasan ya fara buga wa wata kungiya a Kamaru ne lokacin da Arsene Wenger ya gano shi, kuma ya kai shi kungiyar Monaco - a lokacin yana dan shekara 21 da haihuwa.
Daga nan sai ya koma Paris St Germain, da AC Milan da Chelsea da kuma Manchester City - inda ya lashe jerin lambobin yabo.
Amma a daidai wannan lokacin yaki ya daidaita kasarsa Laberiya - yakin da aka kwashe shekara 14 ana yi.
Sabon shugaban ya bayyana karfin gwuiwarsa na cimma nasarori a kan wannan muhimmin aikin.
"Ana kallo na a matsayin tsohon dan wasan tamaula, amma fa ni mutum ne. A ko yaushe ina kokarin ganin na yi fice a dukkan ayyukana.
"Zan iya samun nasarori domin na samu nasarori a aikina na wasan kwallo.
Ko zai iya gudanar da wannan mukamin kuwa ganin cewa siyasa ta banbanta da kwallon kafa?
"Ka san da na bar kasar nan an yi min wannan tambayar? An tambaye ni ko zan sami nasara a Turai.
"Na fada musu cewa idan na yi aiki tukuru kuma na saka zuciyata bisa abin da nake so, na san zan sami biyan bukata."
George Weah zai gaji mulkin kasar da har yanzu ke farfadowa daga annobar cutar Ebola.
Yawancin masu zuba jari da tsohuwar Shugaba Ellen Johnson Sirleaf ta kawo sun tsorata duk da cewa mai kwarewa ce a fagen tattalin arziki daga Jami'ar Harvard.
Katafaren bashin da ta biya da wanda kuma aka yafe wa kasar na kimanin dala biliyan biyar ya fara dawowa kadan da kadan.

No comments:

Post a Comment