Friday, 12 January 2018

An sallami Yusuf Buhari daga Asibiti bayan ya murmure: Shi kadai yayi hadarin babur din: Ba'a kwantar da mahaifiyarshi ba sanadin rashin lafiyar tashi>>Fadar shugaban kasa

An sallami dan gidan shugaban kasa, Yusuf Buhari daga Asibitin da yake kwance dalilin hadarin babur da yayi bayan ya murmure, a wata sanarwa da me magana da yawun shugaban kasar, Femi Adesina ya fitar ya bayyana cewa murmurewa cikin sauri da Yusuf yayine tasa Aka sallameshi daga Asibitin.


Haka kuma sanarwar ta karyata jita-jitar da aka rika yadawa akan hadarin baburdin da Yusuf din yayi, inda aka rika cewa wai bashi kadai yayi hadarin ba shida wani abokinshine Bashir Gwandu, Femi Adesina yace Yusuf shi kadai yayi hadarin babur din.

Haka kuma ya karyata cewar wai ankwantar da mahaifiyarshi, A'isha Buhari dalilin rashin lafiyar dan nata. Saidai abinda sanarwar bata taboba shine maganar sallamar masu tsaron lafiyar Yusuf din da akace an kora daga aikiba dalilin barinshi da suka rikayi yana fita a sace.

No comments:

Post a Comment