Wednesday, 3 January 2018

An yiwa dan shugaban kasa, Yusuf Buhari addu'ar fatan samun lafiya a garin Jos

Kamar yanda ba sabon labari bane, da namiji tilo a gurin shugaban kasa, Muhammadu Buhari, Yusuf Buhari ya samu hadarin babur wanda yayi sanadiyyar samun ciwo akai da kuma karya kafa, Yusuf Buhari dai yana can gadon Asibiti yana jiyya inda Rahotanni suka bayyana cewa har an yimai aiki a kwakwalwarshi amma yana samun sauki.


Kamar dai mahaifinshi, lokacin daya kwanta rashin lafiya, Yusuf din nata samun addu'o'in fatan Alheri daga al'ummar Najeriya, a wannan hoton na sama wata kungiyace a birnin Jos na Jihar Filato suka shirya addu'a ta musamman akan Allah ya baiwa dan shugaban kasar lafiya.

Muna fatan ALlah ya amsa da sauran 'yan Najeriya dake gadajen Asibiti

No comments:

Post a Comment