Wednesday, 3 January 2018

Anyi jana'izar marigayi tsohon gwamnan jihar Kaduna, Lawal Kaita: Gwamnatin tarayya ta aika wakilai

Anyi jana'izar Tsohon gwamanan jihar Kaduna, Marigayi Lawal Kaita a jihar Katsina, yau Laraba, 3 ga watan Janairu na shekarar 2018, Gwamnatin tarayya ta aika da wakilai zuwa jihar ta katsina inda suka mika gaisuwa gurin sakin Katsinar, me martaba Abdulmumini Kabir Usman.Cikin tawagar ta gwamnatin tarayya akwai Ministan harkokin jiragen sama, Hadi Sirika da me magana da yawun shugaban kasa, Malam Garba Shehu da sauran manyan jami'an gwamnati.
Muna fatan Allah ya jikan Lawal Kaita yakai Rahama kabarinshi da sauran Al'ummar musulmi baki daya.

No comments:

Post a Comment