Sunday, 14 January 2018

Anyi yunkurin batawa shugaba Buhari suna amma ya fito ya kare kanshi

Wani sakon shafin yanar gizo na Twitter da aka danganta da shugaban kasa, Muhammadu Buhari da yake nuna goyon baya ga fulani makiyaya dake kashe mutane a jihar Benue ya rika yawo tsakanin mutane amma fadar shugaban kasar ta nesanta kanta daga sakon inda tace makiyan mutane da Allahne kawai suka zauna suka shiryashi.

A wata sanarwa da me baiwa shugaban kasa shawara ta fannin watsa labarai, Femi Adesina ya fitar, yace shugaban kasa muhammadu buhari yana nan akan bakanshi na cewa yayi Allah wadai da harin da aka kai jihar Benue kuma a gano wadanda suka aikatashi dan hukuntasu.

Haka kuma ya nesanta kanshi daga sakon karya dake cewa wai fulanin suna kare kansune kawai a hare-haren da suke kaiwa, ya kara da cewa wadanda suka zauna suka shirya wannan sako makiya Allah da mutanene.


No comments:

Post a Comment