Friday, 19 January 2018

Ayi hattara: Daga bayar da canji an kwashe mishi jarin sayar da doya 8,000

Mugaye da 'yan damfara suna nan suna yawo cikin al'umma kuma suna samun sa'ar mutane ta hanyoyi daban-daban, a dare jiya, Alhamisne, kan tagwayen titunan zuwa Abuja dake Kaduna wani dan damfara ya kwashewa wannan bawan Allahn matashin me sayar da doya jarin dubu takwas, daga bashi canji.Matashin wanda bashi da alamar shaye-shaye ko kuma hauka, an ganshi yanata rusa kuka, hannaye biyu-biyu akai, yanata kaiwa da komowa, yana fadin "Wayyo Allahna kudina sun tafi bani da jarin siyan doya gobe", wannan dalilin yasa hankalin mutane ya karkata zuwa gareshi, bayan ya dan natsu aka tambayeshi abinda ya faru.
Sai yake cewa wanine ya tambayeshi canjin Dubu daya, ya tsaya ya bashi, bayan mutumin ya tafi ya saka dubu dayar cikin sauran kidinshi dubu takwas, wanda sune jarinshi, dama ya gama sayar da doyar zai tafi makwancinshi kenan, kawai sai ya laluba aljisunshi yaji babu kidin sun tafi.
Bawan Allahn ya cigaba da rusa kuka yana ba mutane labari, daga baya daia aka bashi baki yayi shiru, ananne ya tuna cewa ya bar baron doyar tashi can akan titi yaje ya dauko, da 'yan sauran doyoyinshi a ciki.

Wani bawan Allah a gurin ya saye sauran doyar akan naira dubu uku dan ya rage mishi radadi, Matashin dai daga jihar Zamfara yake amma be bayyana sunanshiba.

Allah shi kyauta, ya ahiga tsakanin na gari da mugu.

No comments:

Post a Comment