Wednesday, 17 January 2018

Ayi hattara: Wani ya karya kasusuwan wuya dalilin hana atishawa fitowa

Wani abu da ba kasafai ya cika faruwa ba, ya faru da wani mutum a lasar Ingila, mutumin ya karairaya kashin wuyanshine dana kirji sanadin atishawa da yayi bakinshi da hanci a rufe, be bari iskar ta fito wajeba.


Jaridar Time ta ruwaito cewa mutumin yaje Asibiti inda ya shaidawa likita cewa baya iya hadiya tun bayan da yayi wata atishawa, baki da hancinshi a kulle , koda likitoci suka duba sai sukaga ashe ya karya kashin wuyane ta baya sannan kuma a kirjinshima an samu matsala, wannan abu ya baiwa su kansu likitocin mamaki.

Likita Anthony a asibitin Leicester, yayi kira ga mutane da cewa idan zasu yi atishawa su daina rika rufe hanci ko baki, idan so samune ma bari iskar tana fitowa gaba daya da karfinta, domin a suk lokacin da mutum yayi atishawa to wata cutace yake fitarwa.  

Amma rufe baki da hanci a hana iskar atishawar fitowa, yana sa iskar atishawar ta koma ciki kuma saboda karfinta zata iya karairaya kasusuwan wuya ko na kirji wanda jakan zai iya sanadon mutuwa.

No comments:

Post a Comment