Saturday, 27 January 2018

Ba abin da zai hana ni zuwa Kano>>Kwankwaso

Wani na hannun daman Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso, Comrade Aminu Abdussalam ya ce babu gudu babu ja da baya game da ziyarar da tsohon gwamnan Kanon ya shirya kai wa kano a karshen wannan watan.


Ya ce kwamishinan 'yan sandan jihar Kano ya "Rubuto wa Sanata Kwankwaso cewa suna ba shi shawara cewa akwai wasu mutane da ka ce sun yi shiri za su je su tayar da tarzoma a wurin taron da zai haifar da wani abu mara dadi".

Ya kuma kara da cewa: "Saboda haka 'yan sanda suna ba shi shawara da ya janye zuwansa Kano."

Amma da alama Sanata Kwankwason bai karbi wannan shawarar ta 'yan sanda hannu bibiyu ba:

"A matsayinsa na dan kasa kuma daya daga cikin jagorori na siyasar Najeriya, ya rubuta musa cewa ya ga takardarsu, kuma a iya fahimtarsa, aikin jami'an tsaro ne su tabbatar da tsaro, ba ma nasa ba, amma na al'ummar kasa duka," inji Comrade Aminu Abdussalam.

Ya kara da cewa kamata yayi 'yan sanda su dauki mataki akan wadanda suke kitsa wannan tashin hankalin.

Dangane da ko sun dauki shawarar ta 'yan sanda na cewa su dage wannan taro a Kano, ya ce: "Matsayin da muka dauka shi ne, a bisa doka da tsarin mulkin Najeriya, wajibi ne ga jami'an tsaro da kwamishinan 'yan sanda na Kano ya tabbatar da tsaro ga Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso da ma duk wani mutumin Kano da tabatar da cewa sun yi harkokinsu ba tare da tsangwama ba".
bbchausa.


No comments:

Post a Comment