Tuesday, 16 January 2018

"Bana Fariya">>Adam A. Zango zai bayar da kyautar dubu 100

Tauraron fina-finan Hausa kuma mawaki, Adam A. Zango ya bayyana wadanda suka lashe kyautar kudi daya saka a wata gasa wadda akayi akan sabon fim dinshi me suna Gwaska ya Dawo, a farkon sanarda gasar, Adamun yace wanda ya lashe zai bashi kyautar naira dubu Hamsin, amma a lokacin da yake sanar da wadanda suka lashe gasar yace zai basu dubu darine, wanda hakan ke nuna cewa ya ninka kudin kyautar kenan.


Adamu yace wasu masu sunan Arewa Exclusive ne suka lashe gasar kuma zai basu kyautar kudinne a gurin nuna fim din nashi. Haka kuma yace duk wadanda suka nemi cin wannan kasar daya saka zai basu tikitin shiga kallon fim din nashi kyauta.

Da yake karin bayani a cikin sanarwar daya fitar Adamun yace bawai nuna fariya yake ba a irin wadannan gasar da yake sakawa ba, kawai yanayine dan kara dankon soyayya da zumunci tsakaninshi da masoyanshi da kuma faranta musu.

No comments:

Post a Comment