Sunday, 14 January 2018

"Bance ina son shugaba Buhari da aure ba: Kage akamin">>Fati Shu'uma

Tauraruwar fina-finan Hausa, Fati Shu'uma ta fito ta karyata wani labarin kanzon kurege da ake yadawa akanta, wai tace tana son shugaban kasa Muhammadu Buhari da aure, jarumar tace tabbas tana son shugaba Buhari a matsayin shugaban al'umma na gari amma ba da maganar aureba kamar yanda ake yadawa.


A wani gajeren bidiyo data wallafa a dandalinta na sada zumunta da muhawara, Fati tace wannan magana kagece kawai aka mata "Karyace, karyace, karyace",  kuma tayi kira ga masoyanta da su watsa wannan karyata labari da tayi dan a wanketa daga zargi.

No comments:

Post a Comment