Wednesday, 31 January 2018

"Banga aibun haduwar maza da mata wajan yin fim ba">>Sani Musa Danja

A wata hira da yayi da manema labarai, tauraron fina-finan Hausa da turanci kuma mawaki, Sani Musa Danja, Zaki, an tambayeshi me zaice dangane da irin yanda wasu mutane ke kallon harkar fim dacewa ana abubuwan da basu kamataba a ciki, Sani yace abinda yasa ake yawan ganin laifin 'yan fim, mutane sun saka musu ido da yawane.Ya kara da cewa, zakaga idan aka ce za'a buga wata muhimmiyar kwallo, matasa, maza da mata zasuyi tururuwa su shiga gurin kallon wasan kuma za'a gauraya ba'a damu ba, ba'a magana. Amma idan akazo kan maganar harkar fim, saboda mutane sun zuba ido, dama jira suke suga laifin dan fim sai ayi ta surutai, ya kara da cewa, saboda haka shi baiga damuwa ba a haduwar maza da mata ayi harkar fim ba tunda a sauran al'amura na rayuwa ma mutane maza da mata suna haduwa suyi.


No comments:

Post a Comment