Wednesday, 10 January 2018

Cristiano Ronaldo ya lullube fuskarshi dan badda kama amma be tsiraba

A jiya, Talatane tauraron dan kwallon kafa, Cristiano Ronaldo ya fito daga wani gidan cin abinci mallakin kungiyar da yake bugawa wasa, Real Madrid fuskarshi a rufe da wani mayafi, dabararshi itace kar mutane su gane, amma duk da haka be tasiraba.Yana fitowa daga gidan abincin sai kuwa mutane sukamai caa, domin sun ganeshi kamar yanda jaridar Dailymail ta kasar Ingila ta ruwaito, duk da haka be cire lullubin fuskar tashiba, a haka ya shiga motarshi ya tuka ya tafi.

'Yan wasan kungiyar Real Madrid dai na nuna matukar damuwa bisa tazarar maki dake tsaninsu da babbar abokiyar hamayyarsu, Barcelona dayakai maki shashida a teburin laliga, dan wasan baya na kungiyar, Marcelo ya bayyana cewa abin akwai takaici, sun buga kwallo da kyau sunyi shiri iya shiri amma har yanzu bata canja zaniba.

Saidai kuma a yau, Laraba anga Ronaldon a filin kwallo yana atisaye cikin farin ciki da kwallo, amma maimakon aga yana atisaye da kafa, sai ya rika wasa da kwallon da hannunshi.


No comments:

Post a Comment