Saturday, 6 January 2018

"Da aurena nike fim kamar yadda kowace ma'aikaciya ke aikin office da aurenta">>Daso

Tauraruwar fina-finan Hausa, Saratu Gidaso wadda akafi sani da sunan Daso kuma take fitowa a mafiyawanci, matsayin uwa ko kuma masifaffiya a Fim, ta baiwa masoyanta damar yimata tambaya a dandalinta na sada zumunta da muhawara inda kuma ta amsa musu wasu tambayoyin da aka mata.Mafi yawancin tambayar da mutane sukafi yi shine akan wannan hoton da aka gani na sama, da yawa sun tambayi Dason cewa, shin wai zatayi wani sabon aurene kokuwa, ta bayar da amsar cewa" dama can inada aurena, mun dauki hotone ranar daya ga watan sabuwar shekara muka saka a facebook".

Wani kuma ya tambayeta 'ya'yanta nawa tace
'Ya 'yana hudu'

An tambayeta akan maganar aure da yin fim sai tace
"Kamar yanda kowace mace, ma'aikaciya take da aure kuma take aikinta na office haka nima inada mijina kuma ina zuwa inyi fim"

Wani ya tambayeta shin wai ina gaskiyar cewa tayi aiki da kafar watsa labarai ta DW?, Daso tace " banyi aiki da DW ba, da sashen hausa na bbc nayi aikin wucin gadi lokacin ina karatu a jami'ar Oxford ta kasar Ingila"

An tambayeta wanene jaruminta kuma wacece jarumarta da tafiso, kuma menene burinta nan gaba? Tace" Ai ni uwace kowa nawane, abinda nikeso shine Allah ya horemin kudi da yawa inyita taimakawa na kasa dani"

An tambayeta da wane jarumi tafiso a hadata a fim? Tace " da kowa"

An tambayeta me ta karanta a makaranta tace "sanin halayyar dan Adam"

No comments:

Post a Comment