Friday, 5 January 2018

"Da neman magana na shigo sabuwar shekara">>Inji Nafisa Abdullahi bayan data saka hotunan jarumar fim din Indiya, Tsirara-Tsirara

A yaune tauraruwar fina-finan kasar Indiya wadda akewa lakabi da Deepika ke murnar zagayowar ranar haihuwarta, taurarruwar fina-finan Hausa, Nafisa Abdullahi ta saka wasu hotunan Deepikar da suke nuna tsiraicinta tayi amfani dasu wajan tayata murnar zagayowar ranar haihuwartata.Nafisa dai ta bayyana cewa tana sane ta zabo wadannan hotunan na Deepikar ta saka a dandalinta na sada zumunta da muhawara saboda tawan cewa wasu zasu iya yin magana.

Ta kara da cewa dama kuma ita maganar take nema domin da neman magana ta shigo wannan sabuwar shekarar.
Wani dai ya yiwa Nafisar magana inda yace mata "Mtsww a banza".

Nafisar ta mayar mishi da martani inda tace shima taga yanata yin abu a banza a dandalinshi, garama shi saboda taga yana binta ta kulashi.

Gadai yanda bin ya kasance.
No comments:

Post a Comment