Tuesday, 2 January 2018

Dan shugaban kasa, Yusuf Buhari na kara samun sauki bayan da akamai aiki a kwakwalwa

Wasu gamayyar kungiyar kwararrun likitoci sun bayayana cewa, dan shugaban kasa, Yusuf Buhari yana kara samun sauki bayan da akamai aiki a kwakwalwarshi sanadiyyar hadarin babur da yayi.Shugaban gamayyar likitocin ya shaidawa jaridar The Sun cewa bazasu fadi ainishin halin da dan shugaban kasar yake ciki ba amma bayan da aka mai aiki a kwakwalwa yana nuna alamar samun sauki kuma suna fatan cewa nan gaba zai warke gaba daya.

Shugaban kungiyar gamayyar kwararrun likitocin ya bayyana asibitin da dan shugaban kasar yake kwance, watau Cedarcrest dake babban birnin tarayya Abuja da cewa yana daya daga cikin asibitin kungiyar tasu ta kwararrun likitoci.

Ya kuma bayyana cewa sunawa dan shugaban kasar dama duka iyalan shugaban addu'ar fatan Alheri.

No comments:

Post a Comment